Kwamitin Tsaro MDD, Ya Bukaci Tsagaita Wuta A Sudan Cikin Lokacin Ramadan

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci tsagaita ba tare da wani bata lokaci ba a Sudan a lokacin watan Ramadana dake karatowa. Dafatarin kudirin

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci tsagaita ba tare da wani bata lokaci ba a Sudan a lokacin watan Ramadana dake karatowa.

Dafatarin kudirin da aka gabatar ya samu amincewar kasashe 14 na kwamitin in ban da Rasha wacce ta ce ba ruwan ta.

Daftarin ya bukaci a dakatar da rikicin kasar ba tare da wata wata ba kafin watan Ramadana, tare da kiran dukkan bangarorin dake rikicin su zamna taburin tattaunawa domin kawo karshen rikicin.

A kwanan ne dai hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa rikicin na Sudan kan iya haifar da yunwa mafi girma a duniya.

Hukumar ta WFP, ta ce kimanin mutane miliyan 18 a Sudan ne ke fama da matsananciyar yunwa.

Sudan ta shiga cikin rudani ne a tsakiyar watan Afrilu, lokacin da rikici ya barke, tsakanin sojojin kasar karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah Burhan, da rundunar kai daukin gaggawa ta RSF, karkashin jagorancin Janar Mohammed Hamdan Daglo, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da tilastawa milyoyi tsarewa daga muhallensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments