Search
Close this search box.

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya Ya Amince Da Daftarin Amurka Kan Zirin Gaza

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudirin Amurka kan Gaza Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya a yammacin jiya litinin ya kada

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudirin Amurka kan Gaza

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya a yammacin jiya litinin ya kada kuri’ar amincewa da daftarin kudurin Amurka na neman tsagaita wuta a Zirin Gaza da kuma aiwatar da yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin Falasdinawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da wani sharadi ba.

Mambobin kwamitin na sulhu 14 ne suka kada kuri’ar amincewa da daftarin kudurin da Amurka ta gabatar, yayin da kasar Rasha ta ki kada kuri’ar.

Shawarar Amurka a matakin farko ta kunshi tsagaita bude wuta nan take tare da sakin fursunoni ta hanyar musayarsu da janyewar sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila daga yankunan da ke da yawan jama’a a Gaza, da kuma baiwa fararen hulan Falasdinawa damar komawa gidajensu da muhallansu a yankunan Gaza, ciki har da arewacin na Gaza, da kuma rarraba musu kayayyakin agajin jin kai a ko’ina cikin yankin ga dukkan fararen hulan Falasdinawa da suke bukata.

Bangaren daftarin kudurin ya hada da dakatar da yakin na dindindin domin a sako dukkan fursunonin yahudawan sahayoniyya a Gaza da kuma janyewar sojojin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila  gaba daya daga yankin na Gaza.

Kamar yadda daftarin kuduri ya hada da matakin batun shirin sake gina Zirin Gaza. Sannan kudurin ya yi watsi da duk wani yunkuri na kawo sauyi na al’umma ko yanki a Zirin Gaza, gami da duk wani matakin da zai rage girman yankin na Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments