Kwamandan Rundunar Sojin Sudan Ya Amince Da Duk Wani Tankunkumi Kan Batun Kare Mutuncin Kasarsa

Babban hafsan hafsoshin sojin Sudan ya yi tsokaci game da takunkumin da Amurka ta kakaba masa da cewa; Ba zai yi tasiri a kansu ba

Babban hafsan hafsoshin sojin Sudan ya yi tsokaci game da takunkumin da Amurka ta kakaba masa da cewa; Ba zai yi tasiri a kansu ba

Kwamandan sojojin Sudan kuma shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a kasar Sudan, Laftanar Janar Abdul Fattah Al-Burhan, ya yi tsokaci kan takunkumin da Amurka ta kakaba masa a makon da ya gabata, bisa la’akari da hargitsi da rashin zaman lafiyar Sudan da kuma kawo cikas ga komawa kan tsarin demokradiyya a kasar.

Al-Burhan ya ce: “Ya ji cewa za a kakaba wa shugabannin sojojin Sudan takunkumi, yana cewa, a shirye suke su fuskanci duk wani takunkumi a kan aniyarsu ta gudanar da hidima ga kasarsu, kuma suna maraba da takunkumin.

A nata bangaren rundunar sojin Sudan ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta yi Allah wadai da takunkumin da aka kakaba wa kwamandan rundunarta Janar Abdul Fattah Al-Burhan.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: Rundunar sojin Sudan ta yi Allah wadai da matakin rashin adalci da ma’aikatar Baitul-malin Amurka ta fitar na kakabawa shugaban majalisar gudanar da mulkin a Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Laftanar Janar Abdul Fattah Al-Burhan takunkumi, kuma shugaban al’ummar Sudan da ke jagorantar yakin kare mutuncin kasa, wanda sojojin Sudan da al’ummarta suke kare kasarsu daga ‘yan ta’addar sojojin haya da gungun ‘yan tawayen Muhammad Hamdan Al- Daglo Hamidati, don haka suna yin Allah wadai da batun duk wani matakin da zai iya shafar kowane daga cikin shugabannin sojojin kasar Sudan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments