Search
Close this search box.

Kwamandan Rundunar Sojin Saman Iran Ya Ce: Suna Cikin Shirin Kalubalantar Duk Wata Barazana  

Kwamandan rundunar sojin saman Iran ya bayyana cewa: Ba su gafala da irin barazanar da suke fuskanta ba Kwamandan rundunar sojin saman kasar Iran Birgediya

Kwamandan rundunar sojin saman Iran ya bayyana cewa: Ba su gafala da irin barazanar da suke fuskanta ba

Kwamandan rundunar sojin saman kasar Iran Birgediya Janar Ali Reza Sabahifard ya bayyana cewa: Rundunar sojin saman Iran ta inganta karfin tsaron sararin samaniyar kasarta domin fuskantar barazanar masu girman kai na duniya, yana mai jaddada cewa: Sojojin Iran ba su gafala daga duk wata barazana da sauran makirce-makirce da suke fuskanta ba, kuma suna sa ido sosai kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take gudanar da take-takenta a yankin.

kwamandan rundunar sojin saman kasar ta Iran Birgediya Janar Ali Reza Sabahifard ya tunatar da cewa: Duniya a halin yanzu tana ganin irin zaluncin da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummar Gaza, yana mai jinjinawa irin sadaukarwar da ‘yan gwagwarmaya irin su shahidi Imad Mughniyeh da shahidi Fouad Shukr suka yi, yana mai rokon Allah ya kara daga darajarsu.

Birgediya Janar Sabahi Fard ya yi nuni da cewa: Jami’an rundunar sojin saman Iran suna dubi kan maganganun Jagoran juyin juya halin Musulunci da idon basiri, inda ya jaddada cewa rayuwar al’umma ta dogara ne da karfafa bangarorin iko da tsaron sararin sama a matsayin sahun gaba na kariya ga martabar al’umma da wanzuwarta da kuma kimar al’umma don haka malamai da kwararrun sojojin sama suna bin umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci na wannan sako tare da yin nazari dalla-dalla kan matakin wurin yaƙin tsaron sararin samaniyar kasarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments