Kwamandan rundunar sojin sama ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci Birgediya Janar Amir Ali Haji-zadeh ya sanar da cewa: Wasu kananan garuruwa ne kawai a Iran ba su da sansanin makami mai linzami na karkashin kasa.
Birgediya Janar Haji-zadeh ya yi nuni da cewa: Cibiyoyin makamai masu linzami na Iran suna zurfin mita 500 a karkashin kasa, yana mai cewa: Adadin cibiyoyin makamai masu linzami na Iran suna da yawa ta yadda koda an gano su ba zai yi sauki a tunkare su ba.
Kwamandan rundunar sojin sama na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa, cibiyoyin suna dauke da tarin makamai masu linzami kuma na’urorin leken asiri na zamani ba za su gano su ba.