Hizbullah Ta Sha alwashin tilastawa Isra’ila neman tsagaita bude wuta

Sabon Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce kungiyar za ta ci gaba da tsayin daka wajen tinkarar ta’addancin Isra’ila kuma ta kuduri aniyar tilastawa Isra’ilar kawo karshen yakin da take yi da Lebanon. A yayin jawabinsa na biyu tun bayan nada shi a matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Na’im Qassem […]
Gwamnatin Iran ta ce sakamakon zaben Amurka ba shi da wani tasiri a gare ta

Iran ta ce sakamakon zaben shugaban kasar Amurka da ya nuna Donald Trump na kan hanyarsa ta zuwa fadar White House ba wani batu ba ne a gare ta, duk da cewa zai iya sanyawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran karin takunkumi. A shekarar 2018 ne Amurka, karkashin Shugaba Trump, ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar da […]
Kafofin yada labaran Amurka sun ayyana Trump a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa

Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasar Amurka, inda ya kayar da Kamala Harris. Nasarar da Trump ya samu ta zo ne a bayan yakin neman zabe mafi muni da ak samu a tarihin Amurka. “Nasarar siyasa ce da kasarmu ba ta taba ganin irinsa ba,” kamar yadda Trump ya shaidawa magoya bayansa a Florida. […]
Hamas ta bukaci Trump ya dauki darasi daga kuskuren Biden, ya kawo karshen goyon bayan Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce dole ne sabuwar gwamnatin Amurka ta Donald Trump ta dauki darasi daga kura-kurai na Joe Biden, sannan ta yi aiki da gaske wajen dakile kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar Falasdinu. A cikin jawabinsa na nasara, zababben shugaban ya yi ikirarin cewa “zai kawo karshen yake-yake.” […]
Kwamandan Dakarun Iran Ya Ce: Suna Da Tarin Makamai Masu Linzami Na Fitan Rai

Kwamandan rundunar sojin saman Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya sanar da cewa: Akwai tarin makamai masu linzami a garuruwan Iran don haka makiya ba za su iya kalubalantar kasar ba Kwamandan rundunar sojin sama ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci Birgediya Janar Amir Ali Haji-zadeh ya sanar da cewa: Wasu […]
Fira Ministan Isra’ila Ya Kori Ministan Yakin Yahudawan Sahayoniyya Daga Kan Mukaminsa

Manistan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana dalilai 3 da suka sa aka yanke shawarar korarsa daga kan mukaminsa Yoav Gallant, wanda fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kora daga kan mukaminsa na ministan tsaro, ya yi kira ga gwamnatin yahudawan sahayoniyya da ta yi kokarin dawo da fursunonin yahudawa da […]
Kungiyar Hamas Ta Yi Tsokaci Kan Korar Ministan Yakin Isra’ila Yoav Gallant Daga Mukaminsa

Babban jami’i a kungiyar Hamas ya tsokaci kan korar ministan yakin Isra’ila Yoav Gallant daga mukaminsa amma Hamas tana nan daram Babban jami’i a kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Sami Abu Zuhri, ya yi tsokaci kan korar ministan tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila Yoav Gallant da fira ministan mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi […]
Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya A Falasdinu Ta Ce Kisan Kare Dangi Ake Yi A Gaza

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a Falasdinu ta ce: A bar kiran abin da ke faruwa a Gaza da yaki, domin kisan kare dangi ne tsantsa Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya kan Falasdinu, Francesca Albanese, ta jaddada cewa: Abin da ke faruwa a Gaza dangane da matsalar yunwa wani tsari ne da aka shirya da nufin halaka […]
Harin Sojin Isra’ila Kan Kudancin Lebanon Ya Yi Sanadin Shahadar Mutane 20

Mutane 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani farmaki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan garin Barja da ke kudancin Beirut na kasar Lebanon Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa: Akalla mutane 20 ne suka mutu yayin da wasu 14 na daban suka jikkata sakamakon wani farmaki da jirgin […]
Kan masu jefa kuri’a a Amurka ya rabu kan goyon bayan ‘Isra’ila’: NBC

Yayin da “Isra’ila” ke ci gaba da kai hare-hare kan zirin Gaza da Lebanon, masu kada kuri’a a zaben shugaban kasa na ci gaba da samun rarrabuwar kawuna kan batun shigar Amurka a cewar NBC News Exit Poll. Kuri’ar ta nuna cewa masu kada kuri’a sun kusan rarrabuwa: wasu na ganin goyon bayan Amurka ga […]
Donald Trump na kan gaba a zaben shugaban kasar Amurka

Dan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump na kan gaba a zaben shugaban kasar Amurka bisa ga sakamakon da ke fitowa daga jihohin daban-daban na kasar. Bayanan sun nuna cewa Donald Trump ya da adadin kuri’un wakilai masu zabe 267 yayin da abokiyar takararsa ta jam’iyyar Demokrats Kamala Harris take da 224. Kowane dan takara na […]
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Firayi Ministan Pakistan a Islamabad

Ministan harkokin wajen Iran ya gana da firaministan Pakistan a Islamabad inda suka tattauna kan batutuwa da dama. Abbas Araghchi da Shehbaz Sharif sun tattauna kan kokarin bunkasa alaka da kuma kawo karshen yakin kisan kiyashin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi a Gaza, da kuma wajabcin hana Isra’ila ci gaba da aikata irin wadanann […]
Hezbollah ta harba makaman roka a kan yankin masana’antu na Isra’ila a Haifa

Kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa ta harba makaman roka a kan yankin masana’antu na Isra’ila da ke kudancin Haifa, a wani mataki na ramuwar gayya ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila. Kungiyar Hizbullah ta kuma bayar da rahoton hare-hare kan sansanin Miron da ke gudanar da ayyukan jiragen sama, da kuma sansanin Ma’aleh Golani, cibiyar […]
Tauraron dan adam na Iran Hodhod da Kowsar a cikin sararin samaniya

Masu bincike na wani kamfanin ilmin sararin samaniya na kasar Iran, bayan kera kera tauraron dan adam biyu na “Hodhod” da Kowsar, a ranar Talata 5 ga watan Nuwamba, sun yi nasarar yi musu allurar da jirgin Soyuz na Rasha mai nisan kilomita 500 daga sansanin Vostochniy na kasar Rasha. Tauraron dan Adam na Kowsar […]
Dubban yahudawa sun tare hanyoyi a Tel Aviv domin nuna adawa da korar Gallant

A wata gaggarumar zanga-zangar ba zato ba tsammani da ta barke bayan korar ministan tsaron Haramtacciyar Kasar Isra’ila Yoav Gallant da Benjamin Netanyahu ya yi, dubban yahudawa masu zanga-zanga sun toshe babbar hanyar Tel Aviv – Ayalon, lamarin day a kawo babban tsaiko da cunkoso na ababen hawa. Zanga-zangar ta barke ne a daren jiya […]