Search
Close this search box.

Kungiyoyin Hizbullah Da Kuma Ansarullah Sun Yi Luguden Wuta A Kan HKI

Mayakan kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami samfurin Katusha a kan matsugunan yahudawa a cikin kasar falasdinu da aka

Mayakan kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami samfurin Katusha a kan matsugunan yahudawa a cikin kasar falasdinu da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa a ranar litinin sun cilla makamai masu linzami shamfurin Katusha a kan matsugunan yahudawa a garuruwan Ainu-Yaakub, Ga’otun da kuma Yahi’am  inda suka lalata gidaje da dama sun kuma haddasa gobara mai yawa.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa hare haren sun kai garin Zubaidin da kuma Al-Ramtha na tuddan Kafarshuba da Mazari’u-shiba  na kasar Lebanon da aka mamaye.

A wani labarin kuma sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan cilla makamai kan wani jirgin ruwa a cikin Tekun maliya saboda sabawa dokar hana duk jiragen masu zuwa HKI ta tekun. Labarin ya kara da cewa jirgin ruwan da abin ya shafa shi BLUE LAGOON 01.

Kakakin sojojin kasar Yemen Yahyah Saree ya bayyana cewa sun yi amfani da jiragen yaki masu kunan bakin wake wadanda ake sarrafasu daga nesa don kai hare haren.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments