Shuwagabannin kungiyoyin Hamas da kuma Jahadul Islami sun bukaci kungiyar PLO ta jenya amincewarta da samuwar HKI saboda maida martini ga majalisar dokokin HKI Keness wacce ta kara tabbatarda cewa ba zata taba amincewa da kafuwar kasar Falasdinu a kan kasar Falasdinawa da suka mamaye ba.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta kara da cewa shuwagabannin biyu, Isma’ila Haniya da Khalid Nakhala sun bayyana haka ne a jiya Alhamis a birnin Doha na kasar Qatar inda suka hadu don tattauna al-amura da suka shafi yakin da suke fafatawa a Gaza da sauran yankunan Faladinawa da aka mamaye.
Shuwagabannin kungiyoyun biyu sun yaba da yadda dakarunsu suka jajirce kuma suke ci gaba da jajircewa a yakin da suke fafatawa da sojojin HKI a Gaza. Sun bayyana yakin Tufanul aksa a matsayin yaki wanda ya cimma burinsa na sanya HKI cikin matsaloli wadanda bata tsammani ba. Daga karshen sun bukaci shugaba Mahmood Abbas na kungiyar gamayyar kungiyoyin Falasdinawa wato PLO ya janye amincewar da kungiyarsa take yiwa samuwar HKI don maida martini ga majalisar Keness ta yahudawan HKI