Kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa sun soki kungiyar Human Rights Watch da bin son zuciya wajen karkata ga kare manufofin Isra’ila a cikin rahoton da ta fitar kan Gaza
A cikin watanni 9 da suka gabata, an samu bayanan kisan kiyashi da Isra’ila take aikatawa a Gaza a kullum, a kan idon duniya.
A cikin irin wannan yanayin ne kungiyar Human Rights Watch ta buga rahoto mai shafuka 280, wanda babu batun kisan kare dangin Isra’ila a Gaza a cikinsa. Rahoton bai mayar da hankali kan yawan mutuwar fararen hula a Gaza ba, da yawan kashe-kashen da ake yi a kowace rana, gawarwakin da suke warwatse a kan tituna, da yara da ke mutuwa sakamakon hari ko kuma yunwa, da mutane sama da 9,000 da aka sace a Gaza, ko kuma rahotanni masu tayar da hankali na azabtarwa da fyade daga gidan yarin Sde Teiman da sauran gidajen yarin Isra’ila.
Rahoton na HRW ya mayar da hankali ne kawai kana bin da Isra’ila ta rawaito tun daga lokacin fara yakin 7 ga Oktoba, wanda kuma a aknsa ne kasashen yamma musamman Amurka ta gina dukkanin zantukanta a kan yakin Gaza.
Rahoton na HRW ya gaza yin cikakken bayani game da yanayin tarihi, wanda ke da mahimmanci don fahimtar dalilan da suka haifar da harin Hamas na ramuwar gayya a ranar 7 ga watan Oktoba a kan Isra’ila, a maimakon hakan rahoton na HRW ya ginu a kan mahanta wadda ke nuna cewa tamkar matsalar Isr’ila da Falastinawa ta fara ne kawai daga harin Hamas na 7 ga Oktoba, tare da yin watsi da dukkanin ayyukan kisan kiyashi da mamaye yankunan Falastinawa, da keta alfarmar wurare masu tsarki na musulmi da ke Falastinu, da sauran munanan ayyuka da suka sabawa dukkanin dokoki bna kasa da kasa da hakkin bil adama da Isra’ila take aikatawa kan Falastinawa tsawon shekaru fiye da 75 da suka gabata.
A lokuta da dama, bangarorin gwagwarmayar Falastinawa sun sha bayyana dalilan da suka haifar da harin guguwar Aqsa, ta fuskar tarihi, siyasa, da kuma take hakkokin bil adama da cin zarafinsa da Isra’ila take aikatawa kan Falastinawa tun daga shekara ta 1948.