A wasannin kokawa na gargajiya da ake yi a kasar Kyrgyzstan ‘yan wasan Iran sun sami kyautuka mabanbanta da su ka kunshi zinariya 4, azurfa 3 da kuma tagulla 2.
An bude wasannin gargajiyar na kokawa a birnin Bishkek na kasar Kyrgyzstan daga ranakun 16 da 16 ga watan nan na Afrilu.
“Yan wasan na Iran da su ka sami kyautuka sun hada Sa’id Ismaili a ajin nauyi na kilo 67, sai Nasir Alizadeh a ajin nauyi na 87, sai Muhammad Hadi saruwi a ajin nauyi na 97, sai kuma Amin Mirzadeh a ajin nauyi na 130. Kowane daya daga cikin wadannan ‘yan wasan 4 ya sami kyautar yabo ta zinariya.
Sai kuma wasu ‘yan wasan da su ka hada Puya Dadmarz a ajin nauyi na 55 sai Muhammad Riza Rustami a ajin nauyi na 72, da kuma Rasul Garmsar a ajin nauyi na 82, da su ka sami kyautukan azurfa.
Wadanda su ka sami kyautukan tagulla kuwa sun kunshi Amir Riza Deh Buzurgi, sai Iman Muhammadi,a a jin nauyi na 63.
A jumlace kungiyar ta Iran ta sami maki 200, sai ta kasar Kyrgyzstan da take bi mata da maki 144 sannan kasar japan mai maki 142.