Kungiyar Wasan Taekwondo Ta Guragu Ta Iran Ta Zama Zakara A Asiya Karo Na 10 A Jere

Kungiyar wasan Taekwondo ta JMI kuma guragu, sun zama zakara a wasan taekwondo gurago sun lashe gasar ta Asia karo na 10 a jere. Kanfanin

Kungiyar wasan Taekwondo ta JMI kuma guragu, sun zama zakara a wasan taekwondo gurago sun lashe gasar ta Asia karo na 10 a jere.

Kanfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto cewa an gudanar da gasar ne a kasar Malasiya, kuma yan wasa 107 ne daga kasashe 18 suka sami damar halattar gasar a ranar Jumma’an da ta gabata.

Alireza Bakht da Mamed Haqshenas da kuma Marzieh Nasrollah sun sami lambobin Zinari sannan  Saeed Sadeghianpour, Maryam Abdollahpour, da Amir mohammad Haghitshenas sune suka sami lambobin azurfa.

A yayinda Aylar Jami, Leila Mirzaei, Mohammad Taha Hassanpour, Roza Ebrahimi, Leila Rahimi, da Mehdi Pourrahnama kuma suka sami lamabobin tagulla guda 6.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments