HRW; Kai Hari Kan Gidan Yarin Evin Na Iran Laifin Yaki Ne

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin na Iran laifi

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin na Iran laifi ne na yaki

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta ce: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin da ke birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar 23 ga watan Yuni yana matsayin laifin yaki.

A cikin wani rahoto da ta buga jiya alhamis, kungiyar ta yi bayanin cewa hare-haren da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gine-gine da dama a cikin rukunin, sun kuma kashe mutane akalla 80, a cewar sanarwar da Iran din ta fitar, da suka hada da fursunoni da ‘yan uwansu, da ma’aikatan gidan yari, ba tare da wata tabbatacciyar manufa ta soji ba.

Gidan yarin ya ajiye fursunoni 1,500 a lokacin da aka kai harin, wadanda suka hada da masu fafutuka da ‘yan adawa da dama wadanda kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce gwamnatin Iran na tsare da su ta hanyar keta hakkokinsu.

Hare-haren da aka kai a cikin sa’o’i na ziyara, sun yi barna sosai a dakin da aka kai ziyara, da dakin girki na tsakiya, da dakin shan magani, da kuma sassan da ake tsare da fursunoni ciki har da na ‘yan siyasa, a cewar rahoton kungiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted