Labarun da suke fitowa daga Khan Yunus na arecin gaza na cewa sojojin yahudawan sun kashe mutane masu yawa kamar yadda kakakin kungiyar kula da fararen hula Muhammad Basal ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP .
Sannan a wani bangare kuma hukumar abinci ta duniya na FAO ta MDD ta bada sanarwan cewa, hukumar ta sami motoci 25 dauke da kayakin abinci, amma a lokacinda Falasdinawa a Gaza suka yi cincirindo a kusa da motocin sai sojojin HKI suka fara barin wuta kan mai uwa da wabi, bayan sun wuce shingen HKI dake wurin a birnin Gaza.