Yan majalisar dokokin kasar Lebanon mai goyon bayan kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Lebanon Hassan Fadlallah ya bayyana cewa kungiyarsa tana alfahiri da mutanen kasar Lebanon kan yadda suka fito kwansu da kwarkwatansu a sallar idin layya na bana.
Tashar talabijin ta ALmayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Fadlallsh yana fadar haka a yau Litinin a garin Bintijbel na kudancin kasar Lebanon.
Ya kuma kara da cewa kungiyar Hizbullah a shirye take ta fuskanci sojojin HKI a duk lokacinda suka yi kokarin mamayar kasar Lebanon.
Fadlallah ya kara da cewa, jakdun kasashen yamma ko na kasashen larabawa wadanda HKI take aikowa zuwa kasar Lebanon don neman sasantawa da kungiyarsa, da yakamata su kira ta su kuma fada mata gaskiya kan cewa dakatar da yaki a gaza ne kawai zai dutse wutan yakin da ke faruwa a yanzu a arewacin kasar falasdinu da aka mamaye, sannan dakatar da yaki a gaza ne zai duste dukkan fagagen fama da aka bude kan HKI a yankin.
Dangane da Amurka kuma fadlallah ya bayyana cewa da ta so da ta kawo karshen yakin nan tun farkonsa, a halin yanzun ma in tana so zata yi hakan, don HKI tana sarrafawa ne ta inda gwamnatin AMurka take. Banda haka sojojin HKI suna yaki ne da makaman Amurka da sauran kasashen yamma.
Daga karshen Hassan Fadlallah ya kamma da cewa, kungiyar tana da wasu al-amuran na bammamaki da zasu bayyana nan gaba masu yawa idan wannan yakin ya ci gaba.