Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ta Cilla Makamai Kan Kamfanin Kiran Makamai A HKI

Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun cilla makaman Drones a kan wani kamfanin kira makamai a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye a safiyar

Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun cilla makaman Drones a kan wani kamfanin kira makamai a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye a safiyar yau Laraba.

Tashar talabijin ta Al-mAnar ta kungiyar ta bayyana wani rahoton da dakarun suka fitar wanda yake tabbatar da hakan.

Rahoton ya kara da cewa dakarun na Hizbullah sun yi amfani da makaman Drones ko kuma jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa amma kuma na kunan bakin wake. Kungiyar ta kara da cewa makaman ta sami sami bararsu kamar yadda aka tsara a garin Metula na kasar falasdinu da aka mamaye a shekara 1948.

Daga karshe kungiyar ta bayyana cewa ta kai wadannan hare haren ne don daukar fansa kan kisan wani dan kasar Falasdinu wanda yake zauna a sansanin yan gudun hijira na Qasimia kuda da garin Tyre  daga kudancin kasar mai suna  Mohammed Yousef al-Hassan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments