Kungiyar Hizbullah Ta Kai Hari Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Halaka Soja Da Jikkata Wasu

Sojan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila guda ya sheka lahira wasu 12 na daban kuma sun samu raunuka a wani harin makami mai linzami da aka

Sojan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila guda ya sheka lahira wasu 12 na daban kuma sun samu raunuka a wani harin makami mai linzami da aka kai daga kudancin kasar Lebanon

Rundunar sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da cewa: Sojanta daya ya halaka,yayin da wasu 12 na daban suka samu raunuka sakamakon wasu munanan hare-hare da aka kaddamar daga yankin kudancin kasar Lebanon da makamai masu linzami a safiyar yau Alhamis.

A cewar kafafen yada labarai na yahudawan sahayoniyya; An kai hari da makami mai linzami daga kasar Lebanon tare da tarwatsa wata motar sojin sojojin mamaya a yankin “Tel Hai” da ke yankin Upper Galilee, inda harin ya halaka soja guda tare da raunata wasu 12 na daban, ciki har da uku da suke cikin mawuyacin hali.

Majiyar Lebanon ta rawaito cewa: Sojojin mamayar sun kai hari da bama-bamai na sinadarin phosphorus a kan garuruwan kudanci bayan fashewar makami mai linzamin, domin mayar damartani kan kudancin kasar ta Lebanon daga arewacin Falasdinu da aka mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments