Kungiyar Hizbullah Ta Kai Hari Kan Birnin Haifa Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon ta kai hari kan birnin Haifa na haramtacciyar kasar Isra’ila da makamai masu linzami kirar Fadi 1 a daren ranar

Kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon ta kai hari kan birnin Haifa na haramtacciyar kasar Isra’ila da makamai masu linzami kirar Fadi 1 a daren ranar 7 ga watan Oktoba

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da kai hari kan sansanin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila na Karmel da ke kudancin birnin Haifa a shiyar arewacin kasar Falasdinu da ta mamaye, da makamai masu linzami kirar “Fadi 1”, wanda ya yi daidai da ranar tunawa da kai harin Ambaliyar Al-Aqsa a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta ce: Don nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu masu gwagwarmaya a Zirin Gaza da kuma goyon bayan ‘yan gwagwarmaya da martabarsu, da kuma kare kasar Lebanon da al’ummarta, gami da jerin ayyukan Khaibar na mayar da martani kan hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan fararen hula da kisan kiyashi da makiya yahudawan sahayoniyya ke aiwatarwa, karkashin kiran mun amsa kiranka Ya Nasrallah, ‘yan gwagwarmayar Musulunci sun kai hari da karfe 23:20 na yammacin Lahadi, ta hanyar harba makamai masu linzami na Fadi “1” kan sansanin na Karmel da ke kudancin birnin Haifa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments