Kungiyar Hizbullah Ta Kai Hare Haren Ba Zata Kan Sansanin Sojojin HKI A Arewacin Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai hare haren ba zata kan sansanin sojojin HKI da ke Filon tare da amfani da jiragen yaki na

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai hare haren ba zata kan sansanin sojojin HKI da ke Filon tare da amfani da jiragen yaki na kunan bakin wake wadanda suka sami bararsu kamar yadda aka tsara.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sansanin sojojin HKI ta Filon wanda yake kan iyaka da kasar Falasdinu da aka mamaye yana da rumbun ajiyar makamai, da kuma gidajen kwamandojin sojojin yahudawan.

Labarin ya kara da cewa jiragen yakin sun fada kan wadannan wurare ba tare da kuskuresu ba. Don haka akwai zaton dukkan sojojin yahudawan da suke cikin sansanin ko sun halaka ko kuma sun ji rauni.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata  ne sojojin HKI suka fara yaki da kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa a Gaza, wanda kuma ya sa kungiyar hizbullah ta shiga yakin a ranar 8 ga watan Octoban shekarar da ta gabata don tallafawa Falasdinawa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments