Search
Close this search box.

Kungiyar Hizbullah Ta Ce: Sadaukarwa Ce Ta Sanya Aka Fatattaki Masu Kafirta Musulmi

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Sadaukarwar ‘yan gwagwarmaya da na sojojin Lebanon da kuma na Siriya sune suka fatattaki ‘yan ta’adda Kungiyar

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Sadaukarwar ‘yan gwagwarmaya da na sojojin Lebanon da kuma na Siriya sune suka fatattaki ‘yan ta’adda

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Labanon ta tabbatar da cewa: Sadaukarwar da dakarun kasar Lebanon suka yi, da sojojin kasar ta Labanon, gami da sojojin larabawa na kasar Siriya sune suka yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi daga kan iyakokin kasar ta Lebanon, tare da ‘yantar da su a karo na biyu bayan ‘yantar da yankin kudu daga daudar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullahi ta fitar a wajen bikin cikan shekaru bakwai da samun nasaran ‘yancin kai na biyu: Wanda ya zo daidai da ranar ashirin da takwas ga watan Agusta da ke wakiltar nasarar da al’ummar kasar Lebanon da sojojinta da kuma ‘yan gwagwarmayarta suka samu a kan kungiyoyin ‘yan ta’adda masu kafirta ‘yan uwansu musulmai, inda suka kore su daga kan iyakar kasar Lebanon. Wannan lamari ne mai cike da tarihi da ke dauke da manufar hadin kan kasa a cikin mafi kyawun yanayinta.”

Kamar yadda a cikin wannan lamari aka samu mafi daukakan darasi da abin lura wajen kalubalantar makiya ‘yan mamaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments