Search
Close this search box.

Kungiyar Hamas Ta Zabi YahyaSinwar Ya Maye Gurmin Isma’il Haniyya A Mtsayin Shugaban Kungiyar A Bangaren Siyasa

Kungiyar Hamasa wacce take gwagwarmaya da HKI a Gaza ta zabi Yahya Sinwar a matsayin sabon shugaban kungiyar a bangaren siyasa, kuma shi ne ya

Kungiyar Hamasa wacce take gwagwarmaya da HKI a Gaza ta zabi Yahya Sinwar a matsayin sabon shugaban kungiyar a bangaren siyasa, kuma shi ne ya maye gurbin Shahid Isma’il Haniyya wanda HKI ta kashe a ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata a masaukinsa da ke Tehran.

Haniyya dai ya je Tehran ne don halattar bukin rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan,  kuma yahudawan sun kashe ne kwana guda bayan bikin.

Kafin haka dai Yahyan Sinwar shi ne mai kula da yankin zirin gaza tun lokacinda aka nada Haniya a matsayin shugaban kungiyar a cikin watan Fabrairin  shekara ta 2017.

Banda haka Sinwar yana daga cikin jerin Falasdinawa wadanda Yahudawan suke nema, saboda shi ne ya shirya yakin Tufanul Aksa a gaza a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023, wato watanni 10 da suka gabata. Har kuma ta sanya ladar  ga duk wanda ya kamashi ya mikawa HKI.

Osama Hamdan wani jigo a cikin kungiyar yace Sinwar dan shekara 61 a duniya ya sami amincewar dukkan shuwagabanin Hamas kafin su maye gurbin Haniya da shi a jiya Talata.

Hamdan ya kammala da cewa Sinwar zai maye gurbin Haniyyar a matsayin shugaban tawagar tattaunawa a yakin da kungiyar ta ke yi da HKI a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments