Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta fitar da wani kuduri kan kutse sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankunan cikin kasar Siriya
Majalisar kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a matakin wakilan dindindin ta gudanar da wani zaman taro domin samar da matsaya guda daya na larabawa dangane da matakin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka dauka na mamaye karin yankunan tuddan Julan na kasar Siriya da suka mamaye.
A cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar: An gudanar da zaman taron majalisar kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ne bisa shawarar kasar Masar da kuma hadin gwiwar kasashen Larabawa da dama, da nufin daukar matsaya guda daya na larabawa dangane da hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan kasar Siriya.
Zaman taron dai ya haifar da fitar da wani kuduri na Larabawa wanda ke yin Allah wadai da kutsen sojojin Isra’ila da suka yi a yankunan da suke kan iyaka da Jamhuriyar Larabawa ta Siriya da wasu jerin wuraren da suke makwabtaka da tsaunin Hermon da yankunan Quneitra da birnin Damascus, bisa la’akari da hakan a matsayin saba wa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Siriya da gwamnatin mamayar Isra’ila a shekarar 1974.
Kudurin na Larabawa ya jaddada cewa: Yarjejeniyar da aka ambata tana nan tana ci gaba da aiki bisa kuduri mai lamba 350 da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a wannan shekarar, don haka wannan yarjejeniya ba ta shafi sauyin siyasa da kasar Siriya ta samu a halin yanzu ba.