Bayanin da babban bankin kasar ta Najeriya ya fitar, ya bayyana cewa an sami wannan koma bayan ne a cikin makwanni uku da su ka gabata.
Bayanin na babban bankin na Najeriya ya ci gaba da cewa, kudaden ajiyar Najeriya na waje da a cikin watan Disamba sun kai dala biliya 40,887, sun ragu, sun zama dala biliyan $39.723 daga ranar 31 ga watan Janairu 2025.
An bayyana koma bayan ne a kudaden waje na ajiya da babban bankin kasar yake da su, da ya kamata ace a ranar 4 ga watan Febrairu ne za a fitar da kididdiga akan halin da kudaden wajen suke ciki,amma ba a yi ba.
Bugu da kari wannanbayanin ya fito ne daga kamfanin dake kula da kai da komawar kudaden Waje Bismack Rewane da yake hasashen samun raguwar kudaden ajiyar na Najeriya a tsakanin shekarar 2025-2026 sai sami koma baya da kaso 11.47,wato zuwa dala biliyan 36.21, yayin a a cikin shekarar 2026 zai zama dala biliyan 37.65,alhali a 2024 ya kasance dala biliyan 40.9.
Farashin Naira idan aka kwatanta ta da Dala, a 3 ga watan nan na Febrairu shi ne ; Naira 1,500.