Kremlin: Rasha a shirye take don fadada hadin gwiwa da Iran a dukkanin fannoni

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya sanar a wannan  Litinin cewa, kasar Rasha a shirye take ta fadada hadin gwiwa da Iran a dukkan fannoni,

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya sanar a wannan  Litinin cewa, kasar Rasha a shirye take ta fadada hadin gwiwa da Iran a dukkan fannoni, yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana ci gaba da kara habaka, da kuma  amincewa da juna.

Peskov ya yi nuni da cewa, Moscow na goyon bayan ci gaba da shawarwari kan yarjejeniyar nukiliyar Iran, yana mai jaddada cewa, “Matsayar da kasashen turai suka dauka game da batun Shirin Iran na nukiliya ba ta da amfani, kuma hakan  yana kara  dagula lamurra, da kuma kawo cikas ga  duk wani ci gaba na hakika kan wannan batu.” In ji shi.

Wannan matsayi na Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da lamurra suke kara rincabewa a fagen siyasar duniya, da hakan ya hada da halin da ake ciki a yakin Ukraine, da irin matakan da NATO ke dauka a kan batun wannan yaki wajen tunkarar Rasha, da kuma shirin nukiliya na Iran.

Moscow na neman ganin an kara karfafa dangantaka tsakanin da Tehran, da kuma ci gaba da tattaunawa da Washingtona daya bangaren domin sassauta rikice-rikice a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted