Kasar Koriya ta Arewa a karon farko ta baje hotunan cibiyar tache makamashin Uranium na kasar, tare da nuna shugaba Kim Jong-Un na kasar yana zagayawa a cikin masana’antar ana masa bayanin yadda ake tache makamashin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto tashar talabijin ta kasar Koriya ta Arewa ta na bayanin ziyarari da shugaban kasar ya kai cibiya ko masana’antar tache makamashin.
Ta kuma bayyana shugaban yana fadawa ma’aikata masu aiki a cibiyar da su gabatar da sabbin na’urorin tashe Uranium a cibiyar don bawa kasar damar samar da makaman Nukliya saboda kare kanta daga makiya.
Labarin bai inda cibiyar yake a cikin kasar ba, da kuma lokacinda shugaba Kim ya kai ziyarar aiki a cibiyar ba. A shekara ta 2006 ne kasar Koriya ta Arewa ta gwada makaminta na Nukliya a karon farko. Kuma da alamun tana kara kyautata ayyukan cibiyar saboda tafiya da zamani, banda haka kasar ta kore a kare makamai masu linzami masu cin karami da dogon zago. Banda haka ta sha gwadasu don tabbatarwa makaiya kasar kama daga koriya ta kudu da babbar kawarta Amurka irin karfin soje, musamman na makaman nukliya da take da su.