Gaza: Falastinawa 48 Suka Yi Shahada A Hare-Haren Isra’ila

Akalla Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a Falasdinawa

Akalla Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a

Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a.

Majiyoyi a asibitocin Gaza sun bayyana cewa: Shahidai 27 ne a kai zuwa asibitin Al-Shifa, shahidi daya zuwa asibitin Al-Ma’amoudiya, shahidai uku zuwa asibitin shahidan Al-Aqsa, da shahidai biyar zuwa asibitin Nasser.

Wani Falasdine ya yi shahada kana wasu kuma suka jikkata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai hari a wani gida da ke unguwar Sheikh Radwan da ke arewacin birnin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments