Keta Alfarmar Kasar Siriya Da Isra’ila Keyi Babbar Barazana Ce Ga Zaman Lafiyar Yankin

Jakadan iran kuma wakilinta na din din din a majalisar dinkin duniya yayi gargadi game da mamaye yankuna a kasar siriya da Isra’ila ke yi,

Jakadan iran kuma wakilinta na din din din a majalisar dinkin duniya yayi gargadi game da mamaye yankuna a kasar siriya da Isra’ila ke yi, da kuma zalunci kan kasar ta larabawa, yana barazana ga zaman lifya da tsaron yammacin Asiya.

Amir Said Iravani da yake bayani a gaban kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a jiya Alhamis ya ce tun a shekarar bara aka tabbatar da cewa isra’ila ta na yin amfani da karfi da ya sabama doka wajen kara fadada karfin sojanta da kuma kara mamaye yankuna a kasar sirya.

Haka zalika Iravani yayi tir da harin da isra’ila takai a watan jiya a garin beit jinn dake gefen birnin Damaskas  da ya kashe mutane 13 tare da jikkata wasu guda 25 kuma ya bayyana shi a matsayin laifin yaki bisa dokokin kasa da kasa.

Daga karshe yayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da ya dauki tsauraran matakai na tilastawa gwamnatin mamaya da ta mutunta martabar kasar sirya da kuma iyakokinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted