Jiragen yakin kawancen Amurka da Burtaniya a tekun maliya sun kai sabbin hare hare a yankin Attahaita na lardin Hudaida dake yammaciun kasar Yemen a safiyar yau Talata.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa har yanzun ba’a bayyana irin asarorin da hare haren suka jawo ba.
Kasashen Amurka da Burtaniya dai sun samar da kawance wasu kasashen a cikin Tekun Maliya don abinda suka kira dawo da zaman lafiya a mashigar ruwa ta Babul-Mandab na kasar Yemen ga jiragen ruwan HKI.
Kafin hare haren na safiyar yau Talata dai sojojin kasar Yemen sun cilla makamai masu linzami kan wasu jiragen ruwa wadanda suke wucewa da mashigar ruwan, kuma suke nufin HKI.
Gwamnatin kasar Yemen ta sha alwashin ci gaba da hana dukkan jiragen ruwa na HKI ko kuma wadanda suke nufin haramtacciyar kasar har zuwa lokacinda sojojin HK suka daina kai hare hare kan mutanen Gaza.
Tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ne, sojojin HKI ta sama da kasa da ruwa suke ruwan wuta kan Zirin gaza, inda ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa fararen hula kimani 33,000 sannan ta jikata wasu 76,000.