Kawancen kasashen 3 da su ka hada Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar NIjar, sun yi watsi da wa’adin da kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afirka ta zayyana musu na komawa cikin cikinta, tare da bayyana shi da cewa wani kokari ne na hargitsa sabuwar kungiyar da su ka kafa.
A makon da ya shude ne dai kungiyar ta ECOWAS, ta yi wani taro a birnin Abuja, inda ta bai wa kungiyarkasashen uku wa’adin watanni 6 da su sake tunani akan matakin da su ka dauka na ficewa daga cikinta.
Sanarwar da kasashen uku su ka fitar ta ce; Wannan sabon matakin da kungiyar ta dauka, aikin Faransa ne a ‘yan-korenta da zummar sake maimaita hargitsa zaman lafiyar kasashen uku.”
Bugu da kari, kungiyar kasashen uku ta ce, su fa tun tuni sun riga sun bayyana cewa, sun yi wa kungiyar ECOWAS saki uku babu komiya.
Wadannan kasashen uku sun kafa kawance ne a karkashin tsarin kwanfedaliyya, suna kuma yi wa kungiyar ECOWAS kallon wani makami na Faransa da sauran kasashen mulmin mallaka. Bugu da kari, suna ganin cewa kungiyar ta tashi daga kan wacce aka gina bisa shawarwari, zuwa ta kama-karyar wasu mambobi ‘yan tsiraru.