Ministocin harkokin wajen 5 na kasashen larabawa tare da hadin gwiwar jami’an Falasdinawa sun rubuta wa ministan harkokin wajen Amurka Marco Antonio Rubio wasiki da a ciki suke nuna kin amincewa da shirin korar Falasdinawa zuwa wajen Falasdinu.
Kasashen da su ka rubuta wasikar sun kunshi Saudiyya, HDL, Katar, Masar da Jordan, sai kuma mai bai wa shugaban gwamnatin Falasdinu shawara Husain Sheikh, sun kuma mika wannan wasikar ne ga mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Amurka mai kula da yankin gabas mai nisa.
A ranar 25 ga watan Janairu da ya shude, shugaban kasar Amurka ya gabatar da shawarar cewa kasashen Masar da Jordan su karbi bakuncin Falasdinawa daga Gaza.
Tare da cewa Trump din ya ce zaman na Falasdinawa na wani dan karamin lokaci ne,sai dai kasashen larabawan biyu sun ki amincewa da hakan.
Haka nan kuma wasikar ta yi kira da a dauki matakan sake gina Gaza da yaki ya lalata, domin su ci gaba da rayuwa akan kasarsu.
Dangane da makomar Falasdinawa, jami’an diplomasiyyar na Larabawa sun bukaci yin aiki da gwamnatin Donald Trump domin kafawa Falasdinawa kasarsu mai cin gashin kanta.