A gefen taron OIC wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Banjul na kasar Gambiya ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Hussain Abdullahiyan ya gana da tokwaransa na kasar Masar Sami Shurkri inda bangarorin biyu suka gina tattaunawarsu kan wadanda suka gabata a wasu tarurruka a bayan.
Kafin haka dai shugaban kasar Iran sayyid Ibrahim Ra’isi ya gana da tokwaransa na kasar Masar Abdulfattah Assisi a birnin Riyad na kasar saudiya.
Har’ila yai jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun gana a Geneva da kuma birnin NewYork a taron shekara shekara na MDD. Sun kuma bukace a maida huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu, bayan kastewa na shekaru fiye da 40 da suka gabata.
Jim kadan bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran ne, dangantaka tsakanin kasashen biyu ta tabarbare kan rikicin kasar Falasdinu da aka mamaye da kuma matsayin da ko wace kasa take dauke kan rikicin.