Kasashen Iran Da Belarus Sun Cimma Matsaya Akan Aiki Tare Ta Fuskar Musayar Kudade Da Bankuna

A birnin Minsk na kasar Belarus an yi taro karo na 19 dangane da aiki tare a fagen tattalin arziki a tsakanin kasar mai masaunin
Birnin Minsk

A birnin Minsk na kasar Belarus an yi taro karo na 19 dangane da aiki tare a fagen tattalin arziki a tsakanin kasar mai masaunin baki da Kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Manyan tawagogi ne dai su ka wakilci kasashen biyu da su ka fi mayar da hankali akan hanyoyin bunkasa aiki a tsakanin Bankuna da kuma inganta hanyar musayar kudade.

Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya ce; babban bankin Iran ya sami wakilcin Hussain Kashiri wanda shi ne manaja na alakar kasa da kasa, inda ya tattauna da takwarorinsa na Blarusia na tsawon kwanaki 4 a jere akan batun alakar Bankunan kasashen biyu.

A yayin tattaunawar Kashiri ya bijiro da damammakin da Iran take da su ta fuskar tattalin arziki,sannan kuma ya kara da cewa  Bankunan kasar suna cikin Shirin aiki domin jawo hankalin masu zuba hannun jari daga kasar Blarusia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted