Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu.
An rattaba hannu kan takardar ne a gaban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ministar harkokin wajen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Teresa Kayumba, da na Rwanda Olivier Nduhungirehe.
Yarjejeniyar da Amurka da Qatar suka wakilci shiga Tsakani ta hada da tanade-tanade kan mutunta yankunan kasa, haramta ayyukan soji, kwance damarar makamai da hadewar kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da kuma samar da wani tsari na hadin gwiwa don daidaita al’amuran tsaro.