MA’aikatar harkokin wajen kasar Venezue ta sanar da cewa; Abinda Amurkan ta yi sata ce a tsakar ranar Allah da ta yi wa dukiyar al’ummar Venezueal, tare da cewa za ta dauki dukkanin matakan da su ka dace domin sake dawo da jirgin saman nata.”
Sanarwar ta kuma zargin ministan harkokin wajen Amurka Marco Robio da cewa shi ne ya bayar da umarnin kwace jirgin na Venezuela. Haka nan kuma ta kara da cewa; Kiyayyar da Robio yake yi wa kasar Venezuela ce ta sa shi kwace jirgin, da hakan ya mayar da shi zama barawon jiragen,alhali a baya, ba shi da wani aiki sai cusa kiyayya da gaba.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Venezuela ta bukaci ganin an dawo ma ta da jrigin samanta da gaggawa.
Amurka dai ta kwace jirgin saman kasar Venezuela ne da ya sauka a kasar Dominican, bisa zargin yana da alaka da kamfanin man fetur na kasar. Tun a 2019 ne dai Donald Trump ya rattaba hannu akan dokar haramta haramta mu’amala da kamfanin man fetur din na kasar Venezueal (PDVSA)
Wannan dai ba shi ne karon farko da Amurkan take kwace dukiyar kasar Venezuela ba, domin a shekarar da ta gabata ma ta kwace wata matatar mai mallakin Venezuela dake cikin kasar ta Amurka.