Ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria wacce ta fitar da wani bayani ta yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su yunkura domin hana HKI cigaba da aikata laifukan yaki a Falasdinu.
Sanarwar ta ma’aiakatar harkokin wajen Syria ta cigaba da cewa; Abubuwan da ‘yan sahayoniyar suke yi yana cin karo da dokokin kasa da kasa da kuma na MDD.
Bayanin ma’aikatar harkokin wajen na kasar Syria ya kuma ce; A daidai lokacin da mafi yawancin kasashen duniya suke yin tir da abinda yake faruwa a Falasdinu, sai dai kuma har yanzu ba shi da wani tasiri akan matakan da ‘yan sahayoniyar suke dauka na kisan kiyashi.
Cigaban sanarwar ma’aiaktar harkokin wajen kasar ta Syria ya kuma kunshi cewa; Lokaci ya yi da kasashen duniya za su dauki shugabannin ‘yan sahayoniya a matsayin masu aikata laifi haka nan sojojinsu.
Daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa yanzu adadin shahidan Falasdinawa da ya kai 37,000 da 500.