Search
Close this search box.

Kasar Rasha Ta Jaddada Rashin Yiwuwar Murkushe ‘Yan Gwagwarmaya Musamman Na Falasdinu

Bayani mai zafi daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha dangane da neman murkushe gwagwarmayar Falasdinawa Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fada a jiya

Bayani mai zafi daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha dangane da neman murkushe gwagwarmayar Falasdinawa

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fada a jiya Asabar game da rikicin Falasdinu da Isra’ila mai cike da tarihi cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta iya magance dukkan batutuwa da karfi ba.

Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya ci gaba da cewa: Ba za a yi galaba a kan gwagwarmayar Falasdinawa ba, kuma gwagwarmayar tana ci gaba ba tare da yin kasa a gwiwa ba yau tsawon shekaru 76 tun bayan da ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya suka mamaye yankunan Falasdinawa a shekara ta 1948 a lokacin da Falasdinu take karkashin daular Birtaniya.

Birtaniya ta sayar da daular Larabawa ta Falasdinu ga ‘yan Sahayoniyya karkashin sanarwar Balfour a shekara ta 1917 a karo na farko kuma a karo na biyu ga Daular Birtaniya ta samu kudaden da ake bukata don cin nasara a yakin duniya na biyu da Jamus ta Hitler.

Lavrov ya kara da cewa: Dalilin da ya janyo gazawar Isra’ila na karya lagon gwagwarmayar Falastinawa shi ne, kungiyar Hamas tana wakiltar al’ummar Falasdinu ne wajen neman ‘yancinsu, haka nan kungiyar Hizbullah tana wakiltar gwagwarmayar al’ummar Lebanon da ke son ‘yantar da yankunan kasarsu na kudancin Lebanon da haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments