A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji
Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce: ya kamata mu yi dubi kan lamarin, “Idan har da gaske ne, to wannan shi ne mataki da zai sanya Kyiv ta nemi cimma yarjejeniyar zaman lafiya.”
Peskov ya kara da cewa Da ma Amurka ce ke sahun gaba wajen samar wa da Ukraine makamai. “Don haka idan ta daina ko ta dakatar da bai wa Ukraine agajin soji, to shi ne abin da yafi dacewa kuma shi ne zai kawo zaman lafiya,” a cewarsa.