Abdoulaye Diop, ministan harkokin wajen kasar Mali ya yi kira ga kasashen musulmi su hada kai don su iya warware matsalar al-ummar Falasdinu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a taron kasashen musulmi karo 15 wanda aka gudanar a birnin Banjul na kasar Gambiya a ranakunan 4-5 na watan mayun da muke ciki.
Ministan ya nuna damuwarsa ga abinda yake faruwa a kasar Falasdinu da aka mamaye, ya kuma bukaci hadin kan kasashen musulmi da farko, sannan sauran kasashen duniya don kawo karshen kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza.
Daga karshe ministan yana ganin samar da kasar Falasdiunu mai zaman kanta, tare da kasar Isra’ila zai iya warware matsala tsakanin al-ummun biyu.