A dai dai lokacinda jiragen yakin HKI suke ruwan boma bomai da sama a garin Rafah na kudancin Gaza, sojojin yahudawam a kasa suna yaki mai tsanani da dakarun Falasdinawa a cikin sako sako da lunguna na garin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jami’an gwamnatin Hamas a asbitin Kuwait dake Rafah, sun bada sanarwan shahadar Falasdinawa a fafatawan jiya da dare zuwa safiyar yau sannan wasu da dama sun ji rauni.
Garin rafah dai yana da mazauna yan asalin garin kimani 640,000 amma yan gudun hijira daga sauran yankunan Gaza kimani miliyon 1.4 suke samun mafaka a garin.
Kimani kwanaki 10 da suka gabata ne sojojin HKI suka mamaye kufar shiga yanzkin Gaza daga Rafah, daga lokacin ne suka fara ludguden wuta kan miliyon falasdinawa da suke garin.
Banda haka Yoav Gallan ministan yaki na HKI ya bayyana cewa zai aika da wasu Karin rundunoni zuwa Rafah don murkushe hamas.
Har’ila yau a dai dai lokacinda yaki yake kara tsanani a gaza ne gwamnatin Amurka ta bada sanarwan fara isar tun 500 na kayakin agaji zuwa gaza, wanda kungiyar Hamas to fito karara ta bayyana cewa mutanen Gaza ba sa bukatar agajin Amurka. Don da ita ne mutanen gaza suke yaki kai tsaye.