Mutane a kasashen duniya da dama suna kara fitowa suna goyon bayan Falasdinawa a gaza, da kuma bukatar a maida HKI saniyar ware.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa daliban Jami’o’ii a Amurka suna kara shigowa cikin harkar tokwarorinsu masu goyon bayan falasdinawa a gaza, don kawo karshen yaki da kisan kare dangin da ake masu tare da taimakon gwamnatin kasar ta Amurka.
Labarin ya kara da cewa a ranar 17 ga watan Afrilun day a gabata ne daliban Jami’ar Colombia a birnin NewYork ne suka fara zaman dirshen a wani wari a cikin Jami’ar, inda suke bukatar Jami’ar ta katse duk huldar ta take da ita da HKI, sannan sun bukaci a kawo karshen yaki a Gaza.
Dagan an sauran jami’o’ii a cikin kasar daya bayan daya suka fara shigowa harkar dalibai masu bore har yanzu an sami jami’o’ii a jihohi kimani 25 a Amurka sun shiga batun goyon bayan falasdinawa a Gaza.
A Jami’ar Colombia bayan da hukumomin jami’ar suka dauki matakan amfani da karfin don tawatsa daliban, sun kara fafada zanga zangarsu da kuma borensu zuwa mamayar babban dakin taro na Jami’ar mai suna ‘Hamilton’ inda suka sauya masa suna zuwa Dakin taro na Hind saboda tunawa da wata yarinya bafalasdinaya wacce sojoji HKI ta Kashe a Gaza tare da iyalanta.
A tarihin Amurka daliban jami’ar Colombia sun mamaye wannan dakin taron a yakin Vetnam don tilastawa gwamnatin kasar dakatar da yaki a kasar, sannan a shekara 1985 sun mamaye dakin taronm don neman a kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar Afirka ta kudu.