Martanin farko a hukumance na Japan game da fashewar na’urorin sadarwar Japan a Lebanon
Babban sakataren majalisar ministocin kasar Japan ya sanar da cewa: “Suna tattara bayanai game da fashewar na’urorin sadarwa na ICOM a kasar Lebanon.”
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto daga kamfanin Icom na kasar Japan cewa: Kamfanin yana gudanar da bincike kan rahotannin fashewar na’urorin sadarwa maras waya mai dauke da tambarin kamfanin a kasar Lebanon.
Da sanyin safiyar jiya, wasu na’urori marasa waya suka fashe a hannun masu amfani da su a birnin Beirut da wasu yankuna na kasar Lebanon. Na’urori da dama sun kasance a cikin gidaje, wanda ya kai ga tashin wuta.
Na’urorin marasa waya da suka tarwatse a yankuna a kasar Lebanon sun kasance nau’in “Icom V82”.
Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a ta Ma’aikatar Kiwon Lafiyar Jama’a ta sanar da cewa; “Sake tashin bom na biyu game da sakamakon tashin bama-bamai na haramtacciyar kasar Isra’ila da ya shafi na’urorin marasa waya a yammacin Laraba, inda mutane goma sha hudu suka yi shahada kuma wasu fiye da mutane dari hudu da hamsin suka raunata.”