Kakakin ma’aikatar masana’antu da kasuwanci da kuma ma’adinai na Iran Sayyid Ruhullah Latifi ya bayyana cewa kasar Iran tana daukar nahiyar Afirka mai kasashen 54 da kuma jama’a mai yawan mutane biliyon 1.3 a matsayin dama ga kasar Iran don fadada karfafa harkokin kasuwanci da su.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Latifi yana fadar haka a taron tattalin arziki karo na biyu tsakanin kasashen Afirka da kuma JMI a jiya a nan Tehran.
Ya kuma kara da cewa a halin yanzu kasar Iran tana kara fadada harkokin kasuwanci da kasashen Masar, Libya, Tunisiya, Djibouti, da kuma Morocco. Sannan ya kara da cewa a halin yanzu matsaloli guda uku ne suke hana ruwa guda a harkokin kasuwanci tsakanin JMI da kasashen Afirka kuma sun hada da rashin sanin hakikanin kamfanonin da mutanen da suke son huldar kasuwanci a bangarorin biyu, samun hanyar sifirin kayayyaki mai sauki tsakanin kasashen da kuma matsalar hanyoyin musayar kudade.