Kasar Iran Ta Yi Gargadi Ga Wadanda Suke Son Farfado Da Kungiyoyin Yanta’adda A Arewacin Kasar Siriya

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi gargadi ga wadanda suke son sake farfado da yan ta’adda masu kafirta musulmi a arewacin kasar Siriya, ta

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi gargadi ga wadanda suke son sake farfado da yan ta’adda masu kafirta musulmi a arewacin kasar Siriya, ta kuma bukaci kasashe wadanda suke makobtaka a kasar ta Siriya da kuma yankin Asiya ta kudu gaba dayansu, su mai da hankalin, kuma su yi shirin murkushe dukkan wani motsin da yan ta’adda za su sake yi a arewacin kasar Siriya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA Na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’e yana fadar haka a jiya da dare. Ya kuma kara da cewa yankunan Adlib da da Halab na kasar Siriya na daga cikin yankunan da kasashe uku wato Iran, Rasha da Turkiyya suka amince ya mai aminci a tarurrukan Astana.

Don haka hare-haren da kungiyoyin yan ta’adda suka kaiwa yanki a cikin yan kwanakin da suka gabata, sabawa wannan yarjeniyar ne, don haka wannan yarjeniyar a halin yanzu tana cikin hatsarin a yi watsi da shi, sannan a sake komawa yaki a yankin. Baqae ya kara da cewa, kasar Iran da sauran kawayenta sun fafata da kungiyoyin yan ta’adda a wannan yankin shekaru 14 da suka gabata, kuma da dama daga cikin wadannan kasashen sun gabatar da shahidai don dawo da zaman lafiya a yakin. Kuma ba zasu amince a sake data wani sabon yaki a yankin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments