Kasar Iran ta yi kakkausar suka kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan sansanonin ‘yan gudun hijira a Gaza
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da ‘yan sahayoniyya suke kaiwa kan sansanonin Falasdinawa da suka rasa matsugunansu da tantunansu a Gaza, ciki har da sansanin Nuseirat, wanda ya yi sanadin shahada da raunata Falasdinawa da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata da kananan yara.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya watsa rahoton cewa: Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da ‘yan ta’addan yahudawan sahayoniyya suke kaiwa kan sansanonin Falasdinawa da suka rasa matsugunansu da tantunansu a Gaza, ciki har da sansanin Nuseirat, wanda ya yi sanadin shahada da jikkatar wasu da dama da ba su ji ba ba su gani ba musamman mata da kananan yara.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana ci gaba da gazawar cibiyoyin kasa da kasa da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wajen tunkarar kisan gillar da ake yi wa Falasdinawa sakamakon cikakken goyon bayan da Amurka ke bai wa ‘yan ta’addar sahayoniyya a matsayin abin kunya. Ya kuma yi kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza, da gurfanar da shugabannin mamaya a gaban kotu da kuma hukunta su kan aikata munanan laifuka.