Kasar Habasha ta kasance kasa ta farko a duniya da ta hana shiga da motocin da suke amfani da man fetur da dizal cikin kasarta
Jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta buga wani rahoto da ke cewa: Kasar Habasha ta hana shigo da motocin da suke amfani da man fetur da dizal cikin kasarta, wanda hakan ya sa ta zama kasa ta farko a duniya da ta dauki wannan mataki.
A cikin rahoton da jaridar ta wallafa ta ce: Tun bayan sauya sheka zuwa motocin masu amfani da karfin wutar lantarki, wasu mutane suka daina jira na tsawon sa’o’i a cikin layukan motoci marasa iyaka a kan titunan birnin Addis Ababa, sakamakon hanyoyin shiga gidajen mai da ke fama da matsalar karancin man fetur. Wadannan mutane sun kasance suna bi umarnin gwamnatin Habasha na siyan mota masu amfani da wutar lantarki a tun farkon shekara ta 2024, inda suke bayyana cewa: Suna da wadataccen lokaci a fagen rayuwarsu kuma sun daina biyan kudin man fetur.
Tun a watan Janairu ne, ma’aikatar sufuri ta yanke hukunci mai tsauri na hana shigo da duk wasu motocin masu amfani da man fetur da dizal a cikin kasar. Sakamakon haka, aka tilastawa direbobin Habasha canza aniyarsu da amfani da man fetur zuwa motocin lantarki. Wani abin mamaki mutane da dama a kasar ba su samun wutar lantarki kan haka, Yizengaw Yetayeh, kwararre a ma’aikatar, ya ce: Wannan ƙa’idar tana dauke da tsari mai kyau mafi mahimmanci fagen aiwatar da dabarun tattalin arziki. Ya kara da cewa: Wannan doka zata taimaka wajen samun saukar farashin kudaden waje.