Karin Kudin “Data” A Najeriya Ya Fusata Mutanen Kasar Dake Fama Da Matsananciyar Rayuwa

 Mutanen Najeriya suna  bayyana fushinsu akan kara kudaden sayen cajin shiga kafar sadarwa na Internet –Data- da manyan kamfanoni irin su MTN da Airtel su

 Mutanen Najeriya suna  bayyana fushinsu akan kara kudaden sayen cajin shiga kafar sadarwa na Internet –Data- da manyan kamfanoni irin su MTN da Airtel su ka yi, saboda yadda ake fama da matsalar rayuwa.

Kamfanin MTN shi ne mafi girma a tsakanin kamfanonin samar da hidimomi na hanyar sadarwa, inda a yanzu ake sayar da Giga 15, akan Naira 6,000 bayan da a baya take naira 2,000 ( wato daga dala 1.33-3.99) da hakan yake nufin cewa an rubanya farashin sau uku.

Shi ma kamfanin Airtel ya kara yawan kudaden cajin nashi da kaso mai yawa.

Wannan Karin da kamfanonin su ka yi, ya bakanta ran masu amfani da su, musamman a wannan lokacin da ake fama da yanayi mai tsanani na  tattalin arziki.

Kamfanin MTN ya wallafa sanarwa a shafinsa na X cewa; Karin kudin ya zama wajibi domin gabatar da hidimomi  masu nagarta ga kwastomominsa, tare da neman gafara ga abokan hulda.

Wani daga cikin masu tofa albarkacin baki akan Karin na MNT; ya walllafa cewa; Rubanya kudi har sau uku? Lallai karshen duniya ya zo.”

Ana hasashen cewa Karin da aka yi zai shafi kananan ‘yan kasuwa da suke dogaro da hanyoyin sadarwar masu saukin kudi domin tafiyar da harkokinsu.

Ya zuwa yanzu dai kamfanin Globacom, da shi ne kamfani na uku mafi grima a cikin kasar, bai yi  Karin kudin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments