Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, Dr. Nassri Kan’ani ya wallafa a shafinsa na “X” cewa: “Yan sahayoniyar sun sake tafka wani laifi mai girma a makarantar “Cairo” da take yankin Gaza inda ta kashe fararen hula da dama.
A yayin wannan harin da HKI ta kai, ta kashe Falasdinawa 11 tare da jikkata wasu masu yawa.
Dr. Kan’ani ya kuma kara da cewa: Shirin da duniya ta yi akan laifukan ‘yan sahayoniya da kisan kiyashi,a aikace ya ba sake ba su laisisin su cigaba da tafaka laifuka irin wadannan.
Har ila yau kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran din y ace; Kungiyoyin kasa da kasa sun saki hannuwan mashaya jini su aikata abinda su ka dama a gaza, haka nan kuma ya soki masu rajin kare hakkin dan’adam da cewa su ne ke aikewa da makamai zuwa Falasdinu.
Tun daga 07 watan Oktoba 2023, HKI take yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi a karkashin taimako da ciakken goyon bayan kasar Amurka da wasu kasashen turai.
Ya zuwa yanzu kididdiga ta nuna cewa adadin Falasdinawan da aka kashe sun kai 38,000 da 794. Haka nan kuma wasu mutanen da sun kai 89,000, da 364 su ka jikkata.