Kamfanoni Masu Zaman Kansu Na Kasashen Afganistan Da Iran 28 Ne Suka Kullar Harkar Kasuwanci a tsakaninsu wanda kimarsu kai kimanin dalar Amurka miliyon $500.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ya bayyana cewa, kamfanonin JMI da kuma kamfanoni masu zaman kansu a kasar Afganistan 28 ne suka sanya sannu a kan takardun fahintar juna na kasuwanci wanda kimarsu ya kai dalar Amurka miliyon $451.8 a birnin Kabul babban birnin kasar.
Labarin ya kara da cewa, cibiyar kasuwanci ta kasar Afganistan cewa ta shirya wannan taron wanda ya hada wakilan kamfanonin kasashen biyu a birnin Kabul.
Mahmood Siadat shugaban kwamitin hadin giwa na harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya bayyana cewa, kasashen biyu sun yi amfani da harkokin kasuwancin da ke gudana tsakanin kasashen biyu don cimma fadada harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu. Don fadada harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
A halin yanzu, Iraniyawa yan kasuwa fiye da 180 ne suka birnin Kabul na kasar Afganistan don halattan taron kasuwar baje koli na Abu Hanifa ta kasa da kasa za’a bude a birnin Kabul kuma kai ranar 13 ga watan Octoba yana ci.