Kamfanin kera jiragen sama na ‘Airbus’ ya bukaci duk wadanda suka sayi jiragen sama samfurin A320 ya dawo da shi saboda aiwatar da wata gyra a tsarin tuka jiragen.
Kamfanin dillancin Labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto kamfanin yana bada wannan sanarwan a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa,
Wannan shine karon farko wanda kamfanin yake fuskantar matsala irin wannan, wanda ya sanya ta bukaci a dawo da jirage masu yawa don gyara.
Kamfanin Aie Bus shi ne kamfanin jirage mafi girma a nahiyar Turai kuma a karon farko cikin shekara 55 da suka gabata da fara kera jiragen a wannan karo ne ta fara samun irin wannan matsalar.
Gyaran inji sanarwan kamfanin ya shafi wata manhajan tuki ne wanda yake iya haddasa matsaloli idan ba’a gyara ba. Airbus tana da jiragen kimani 6000 wadanda suke zirga-zirga a kasashen duniya da dama, amma wasu daga cikinsu ne suke da matsalar.
Sanarwan ta ce ana bukatar duk jirgin da abin ya shafa ya dakatar da zirga –zirga har zuwa lokacinda za’a gyara manhajar. A lokacin bada wannan sanarwan dai jiragen Airbus kimani 3000 suna cikin tafiya.