Tsokacin kakakin dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas kan harin da kungiyar Hizbullah ta kai kan gidan fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu
Kakakin rundunar sojin Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Abu Ubaida, ya albarkaci farmakin da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kai kan gidan dan ta’addan yahudawan sahayoniyya fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a birnin Qaisariyya.
Abu Ubaida ya yi nuni da cewa: Wannan farmakin yana aikewa da sako ne ga jagororin masu aikata miyagun laifuka ‘yan mamaya cewa: Ko da za su iya kaucewa fuskantar shari’ar kasa da kasa mai ido daya, ba za su iya kubuta daga azabar ramuwa gayya ta adalcin ‘yan gwagwarmaya ba. Sannan kuma shahadar jagororin gwagwarmaya ba zata taba raunana dakarun gwagwarmaya ba, sai dai kara musu kaimi da azamar kalubalantar makiya ‘yan mamaya.
A safiyar ranar Talata ne jami’in hulda da manema labarai na kungiyar Hizbullah ya sanar a wani taron manema labarai cewa: Kungiyar Hizbullah ce ke da alhakin kai hari kan gidan dan ta’adda fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da ke Kaisariya, inda harin ya ruguza gidan.