Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa;yahudawa mazauna sansanin ‘ Beit Ha’imik” sun yi kaura sun bar matsugunansu, saboda yadda gobara take tashi sanadiyyar makaman da Hizbullah take harbowa.
Bugu da kari makaman na Hizbullah suna yawan tashin gobara a sansanin “Amikah”.
Tashar talabijin ta “12” ta HKI ta bayar da rahoton da yake cewa; masu kashe gobara suna kokarin kashe wutar da ta tashi a sansanonin “Ha’imak’ da “Ushrat” dake yankin Jalil.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto cewa; Tare da cewa a kowace rana ‘yan sahayoniya suna kai hare-hare na dabbanci a Lebanon, sannan kuma sun kasa cimma wata manufa, mayakan Hizbullah sun yi nasarar dakatar da rayuwa a Arewacin Falasdinu dake karkashin mamaya.
Ita kuwa jaridar “Badi’ot Ahranot” ta bayar da labarin cewa; An dauki wadanda su ka jikkata sanadiyyar makaman Hizbullah a garin Nahariya zuwa asibiti.
Da safiyar yau Laraba, mayakan na Hizbullah sun kai hare-hare da makamai masu linzami a kan birnin Haifa da kuma Tel Aviv.